Aikin Hajji: Shugaba Buhari ya nemi Kasar Saudiyya ta yi wa ‘Yan Najeriya rangwame
Mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki Kasar Saudiyya ta nemawa ‘Yan Najeriya sauki wajen samun takardar biza domin shiga Kasar ganin aikin Hajjin wannan shekarar ya karaso.
Shugaban Kasar ya aikawa Sarkin Saudi Arabia Salman Bn Abdul Aziz ta hannun Jakadan Najeriya a Kasar Saudi watau Alkali Isa Dodo. Wata Jami’ar Hukumar aikin Hajji na NASCON Fatima Sanda Usara ta bayyana wannan.
Tsohon Alkalin Alkalai Ambasada Isa Dodo ya mika takardar Shugaban Kasar ne a kasa mai tsarki tare da Jami’in Najeriya da ke Kasar Saudi Muhammad Sani Yunusa da kuma Shugaban Hukumar NAHCON Abdullahi Mukhtar Muhammad.
KU KARANTA:
Shugaba Buhari ya koka da wahalar da ‘Yan Najeriya ke sha idan su ka nemi shiga Saudi wajen aikin Hajji da Umrah a dalilin wasu sababbin dokoki da aka kawo ga masu shiga Kasa mai tsarki. Yanzu dai an shigar da bayanan wasu Maniyyatan.
Najeriya tace ba a sanar da ita game da wannan tsari da aka kawo ba don haka ta nemi a dakatar da wannan shiri. Saudiyya dai na neman a rika daukar bayanan Maniyyata yayin da Najeriya ke kukan cewa yanzu ba ta da wadannan kayan aiki.
A bara dai wani Dan Majalisar Dattawa daga Jihar Sokoto Sanata Ibrahim Abdullahi da wasu Sanatocin kasar sun nemi Hukumar kula da aikin Hajji na kasa watau NAHCON ta rage kudin kujerar aikin Hajji sai dai Hukumar ta NAHCON ba tayi hakan ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng