Kotu ta yankewa tsohon gwamna Nyame hukunci shekaru 11 bayan gurfanar da shi

Kotu ta yankewa tsohon gwamna Nyame hukunci shekaru 11 bayan gurfanar da shi

Da safiyar yau ne Legit.ng ta kawo maku labarin cewa wani babban Kotun Tarayya da ke Abuja zai zauna yau domin cigaba da shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Taraba watau Rabaren Jolly Nyame wanda yayi mulki daga 1999 zuwa 2007.

Mai shari’a, Adebukola Banjoko, na babbar kotun Najeriya dake Gudu, Abuja, na can yana yanke hukunci a shari’ar tsohon gwamnan jihar Taraba, Rabaran Jolly Nyame, da aka gurfanar gaban kotu bisa tuhumar almundahanar kudi, biliyan, 1.6bn, shekaru 11 da suka wuce.

Kotu ta yankewa tsohon gwamna Nyame hukunci shekaru 11 bayan gurfanar da shi
Tsohon gwamna Nyame

An tsaurara tsaro a harabar kotun da kewaye inda ake bincikar ababen hawa dake wucewa ta kusa da kotun a safiyar yau, Laraba.

Shari’ar Nyame ta samu tsaiko ne saboda daga kara da Nyame ya yi tayi, yana kalubalantar cajin da hukumar yaki da cin hanci (EFCC) ke yi masa tun watan Yulin 2007.

DUBA WANNAN: Ana zargin mawaki Dauda Kahutu Rarara da cinye kudin mawakan APC miliyan N100m

Nyame ya isa kotun da misalign karfe 9:02 na safe sanye da kaftan ruwan kasa da hula yayin da alkalin kotun ya shiga dakin sharia’a da misalign karfe 9:40 na safe kuma bayan sauraron wata kara gtuda daya ya umarci a gabatar da karar Nyame da misalign karfe 9:46 na safe.

An fara karanta hukuncin da kotu ta zartar a kan Nyame da misalign karfe 9:51 na safe bayan ya tsaya a akwakun masu na laifi.

A cigaba da karanta hukuncin kotun, Mai shari'a Banjoko, ya ce kotu ta samu Nyame da laifin almundahana da kudin jihar Taraba miliyan N250 da kuma almubazzaranci da wasu miliyan N160m.

Bayan kotun ta tabbatar da samun sa da laifin almundahana da badakala da kudin mutanen jihar Taraba lokacin da yake gwamna, daga shekarar 1999 zuwa 2007, mai shari'a Banjoko, ya yanke masa hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel