Muhimman abubuwa 16 da shugaba Buhari yayi magana akan su yau
A yau ne al'ummar Najeriya suke murnar cika shekaru 19 da fara mulkin dimokuradiyya, da kuma murnar cikar shugaban kasa Muhammadu Buhari 3 akan mulki
A yau ne al'ummar Najeriya suke murnar cika shekaru 19 da fara mulkin dimokuradiyya, da kuma murnar cikar shugaban kasa Muhammadu Buhari 3 akan mulki. A cikin bayanan da shugaban kasar yayi a yau, ya bayyana irin nasarorin da gwamnatin sa ta samu, sannan kuma ya bayyana tsare-tsarensa na shekara mai zuwa.
DUBA WANNAN: Buhari yayi alkawarin rattaba hannu akan dokar bawa matasa damar shiga siyasa
A kasa zaku ga jerin muhimman abubuwa 16 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana a yau.
1. Buhari yace gwamnatin sa tazo ne a dai-dai lokacin da al'ummar kasar nan suke bukatar canji.
2. Ya ce 'yan Najeriya sun tsaya tsayin daka akan muhimman abubuwa guda uku da gwamnatin sa tazo akan su sune; Tsaro, yaki da cin hanci da rashawa da kuma habaka tattalin arziki.
3. Ya bayyana cewa, gwamnatin sa ta ci karfin 'yan ta'addar Boko Haram, sanadiyyar da yasa suka bar wuraren da suka kakkama, sannan kuma saki 'yanmata 106 da suka kama na Chibok da kuma 104 da suka kama na Dapchi, sannan da sama da mutane 16,000 da aka samu damar ceto su daga hannun su.
4. Buhari yace akwai kokarin da gwamnatin sa take a yanzu, da zai bawa al'ummar yankin arewa maso gabashin kasar nan damar sama musu makarantu, asibitoci, dakunan shan magani, ruwan sha mai tsabta, wanda hakan zai taimaka wurin dawo da ayyukan da ake yi a yankin na yau da kullum.
5. Bugu da kari, yace matsalar sace-sacen mutane, rikicin makiyaya da manoma, wanda yayi sanadiyyar rasa rayuka da dukiya da dama a wasu jihohi a kasar nan, gwamnati tana bakin kokarin ta wurin ganin abin yazo karshe, sannan kuma wadanda aka kama yanzu da laifin za'a bincike su wadanda suka saka su, sannan a zartar da hukunci a kansu kaman yanda doka ta tsara.
6. Ya yaba da irin kokarin da mambobin hukumar tsaro na kungiyar hadin gwiwar kasa da kasa da suka hada da kasar Nijar, Benin, Chadi, Cameroon da kuma Najeriya, wadanda suke taimakawa wurin yaki da ta'addanci a yankin arewa maso gabas.
7. Yace gwamnatin sa tana jimamin irin kashe-kashen da ake yi a kasar sanadiyyar ta'addanci da yayi kaka gida a kasar nan, ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewar ba zai saurara ba har sai yaga bayan dukkanin 'yan ta'addar da suke addabar al'ummar kasar nan.
8. Da yake jawabi game da yankin kudu maso yammacin kasar nan, Buhari yace gwamnatin sa tana kokari wurin ganin ta tabbatar da cikakken zaman lafiya a yankuna.
9. Yace ya lura cewa 'yan Najeriya da sauran kasashe na duniya sun fara yaba wa manufofinsa da kuma kudurinsa na yaki da cin hanci da rashawa, yayi kira ga 'yan Najeriya dasu cigaba da bawa gwamnonin su hadin kai domin kawo cigaba mai amfani.
10. A bangaren tattalin arziki kuwa, shugaba Buhari yace gwamnatin sa ta mayar da hankali kan sake bunkasa tattalin arzikin kasar nan, ya kara da cewa manufofin da aka gabatar sun hada da hana shigowa da shinkafa daga kasashen ketare, wanda hakan yana da tasiri babba akan tattalin arzikin kasar.
11. A karkashin shirin gudanar da cigaba ga al'umma da gwamnati take yi, gwamnati ta bawa kimanin mutane 264,269 rancen kudi, a yankuna 4,822 a fadin kasar nan, yayin da a yanzu haka akwai mutane 370,635 da gwamnati zata sake bawa rancen, inji shugaban kasar.
12. Yace a bangaren wutar lantarki kuwa, 'yan Najeriya suna bada rahotanni masu kyau na cigaban da ake samu a kowanne lungu da sako na kasar nan. Ya ce a rahoton da aka samu a shekarar 2017 yanzu haka kasar ta samu 5,222.3mw.
13. Ya bayyana irin gudunmawar da matan Najeriya suke baiwa kasar nan a fannin cigaba da kuma harkar dimokuradiyya, a cikin shekaru uku da suka gabata.
14. Buhari yayi kira ga 'yan Najeriya dasu gujewa maganganu na kiyayya ga juna kuma su zauna lafiya, inda yace Najeriya bazata taba cigaba ba har sai an samu kwanciyar hankali da lumana a cikin al'umma.
15. Shugaban kasar ya bukaci 'yan Najeriya dasu bada hadin kai da goyon baya, domin ganin an gabatar da zabe cikin lumana da kwanciyar hankali.
16. A karshe shugaba kasa Muhammadu Buhari yayi alwashin amincewa da dokar nan da zata bawa matasa damar fitowa a dama dasu a siyasa wato "Not Too Young to Run" a turance
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng