Dubi yadda shahararren jarumi Jet Li ya koma bayan gamuwa da wata cuta
- Shahararren jarumin fina-finan kasar China Jet Li na fama da wata cuta mai wuyar sha’ani da ake kira Hyperthyroidism
- Wani hoton sa dake yawo a kafafen yada labara ya tabbatar da hakan
- Saidai manajan Jet Li ya musanta rahotanni da suka ce jarumin na fama da rashin lafiya tare da nanata cewar babu abinda ke damun jarumin
Wasu hotunan shahararren jarumin fina-finan kasar China, Jet Li, dake yawo a dandalin sada zumunta na nuni da cewar ba ya cikin koshin lafiya ganin yadda ya kwarjale.
A cikin hotunan, Jet Li, ya nuna alamun shan wuya da gajiya baya ga mummunar ramewa day a yi. Tsohon jarumin kuma mai shirya fina-finai ya zama tamkar bas hi ba a cikin hotunan.
Wani shafin samar da bayanai dake dandalin yanar gizo, Wikipedia, ya bayyana cutar hyperthyroidism a matsayin ciwo dake bayyana alamu da suke da banbanci a tsakanin mutane. Alamomin ciwon sun hada da; ramewa, gudawa, kumburi ko fitowar makoko a wuya, saurin bugawar zuciya, kasa yin bacci, yawaita jin zafi fiye da kima da sauran su.
Kokarin tabbatar da cewar jarumin ne a jikin sabbin hotunan ya ci tura bayan da manajan sa, Steven Chasman, ya kafe cewar Jarumin garau yake, babu abinda ke damun sa.
DUBA WANNAN: Wasu mata biyu sun musulunta awurin tafsirin azumi
“Muna godiya da kulawar jama’a a kan Jet Li. Amma ina son sanar da kowa da kowa cewar babu abinda ke damun sa. Babu wata cuta dake barazana ga rayuwar sa. Yana nan lafiya,” a cewar Chasman.
Chasman ya kara da cewar, ba lallai hoto ya samar da bayani a kan halin da mutum ke ciki ba tare da bayyana cewar Jet Li na cigaba da shirya wasu sabbin fina-finai da zai fito a ciki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng