Hukumar Alhazai ta jihar Kaduna ta bayyana adadin kudin kujerun bana

Hukumar Alhazai ta jihar Kaduna ta bayyana adadin kudin kujerun bana

- Jihar Kaduna ta bayyana adadin kudin kujeran hajji na shekarar 2018

- Hukumar kula da jin dadin maniyyata na jihar ta ce kudin kujeran aikin hajjin banan ya kai misalin N1.5 miliyan

- Imam Dantsoho, jami'i mai sa ido a kan harkokin hukumar ya ce an samu ragowar N44,615 inda aka kwatanta da kudin kujera ta bara

Hukumar Alhazai ta jihar Kaduna ta bayyana adadin kudin kujerun bana
Hukumar Alhazai ta jihar Kaduna ta bayyana adadin kudin kujerun bana

Hukumar kula da jin dadin maniyyata na jihar Kaduna ta bayyana adadin kudin kujerar na shekarar 2018. Imam Dantsoho, jami'i mai sa ido a kan harkokin hukumar ya ce kudin kujerar a bana ya kai N1.5 miliyan (N1.490,615.05) kamar yadda hukumar hajji na tarayya (NAHCON) ta fadi a wani rahoto na Premium Times.

KU KARANTA: Tramadol da Kodin: Majalisa tayi doka don hukunta masu safarar haramtatun magungunan

Dantsoho ya bayar da wannan sanarwan ne a ofishin hukumar da ke Kaduna a yau Laraba 23 ga watan Mayu. Ya kara da cewa an samu ragowar N44,615 idan aka kwatanta da kudin kujera a barar wato shekarar 2017.

Dantsoho ya ce: "An cinma matsaya a kan kudin kujera na hajjin bana ne bayan anyi ta lissafi don ganin yadda za'a rage kudin kujerar."

A bana, an bawa kowace jihar daman yanke kudin kujerar ta sannan sai ta mika wa hukumar alhazai na tarayya NAHCON domin amincewa dashi.

A wata rahoton, Legit.ng ta kawo muku labari inda aka ce hukumar NAHCON za ta bayyana kudin kujeran hajjin banan bayan ta gama amincewa da kudaden kujerun jihohi 36 da Abuja da kuma na jami'an hukumomin sojoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel