Wani karamin yaro da mahaifiyar sa ta aika debo ruwa ya fada rijiya a Kano

Wani karamin yaro da mahaifiyar sa ta aika debo ruwa ya fada rijiya a Kano

Wani karamin yaro, Sadi Yusuf, mai shekaru 8 ya rasa ran sa bayan ya fada wata rijiya a yau, Talata, a unguwar Tamburawa Gabas, dake karamar hukumar Kumbotso a Kano.

Kakakin hukumar kwana-kwana a jihar Kano, Saidu Mohammed, ya sanar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na (NAN), y ace lamarin ya faru da misalign karfe 7:30 nja safiyar yau.

Ya kara da cewar yaron ya fada rijiyar ne bayan mahaifiyar sat a aike shi ya debo mata ruwa a rijiyar.

Wani karamin yaro da mahaifiyar sat a aika debo ruwa ya fada rijiya a Kano
Rijiya

Da sanyin safiyar yau ne mai unguwar Tamburawa, Isa Garba, ya kira ofishin mu tare da sanar da mu cewar wani yaro ya fada rijiya. Muna samun kiran, muka aika jami’an mu inda suka samu yaron cikin mawuyacin hali. Ya mutu yayin da jami’an mu ke kokarin ceton rayuwar sa,” a cewar Mohammed.

DUBA WANNAN: Gobara ta kone dakuna 12 da shago 1 a garin Kano

Mohammed ya shawarci iyayen yara das u ke gine bakin rijiyar su domin takaita afkuwar hatsari.

A wani labarin Legit.ng kun ji cewar, an hana jami’an manema labarai shiga wurin taron da aka da aka yi tsakanin Oshiomhole da Sanatocin jam'iyyar APC da ranar yau, Talata.

Ziyarar Oshiomhole ga Sanatocin jam’iyyar APC ba zata rasa nasaba da kudirin sa na son zama shugaban jam’iyyar na kasa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng