Lalaci: Wani magidanci ya yi wa matarsa duka saboda ta gaza ciyar dashi
An gurfanar da wani cima zaunen magidanci mai shekaru 47, Olakunle Adebayo a gaban kotun majistare da ke Legas bisa zarginsa da zanne matarsa da belt.
Ana tuhumarsa da aikata laifuka guda biyu wanda suke da alaka da zalunci.
Dan sanda mai shigar da kara, Saja Friday Mameh ya shaidawa kotu cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Mayun 2018 misalin karfe 7.30 ma yamma a gida mai lamba 16 layin Ikota a Lekki legas.
Ya cigaba da cewa wanda ake zargin ya zanne matarsa mai suna Mrs. Tolulope Adebayo ta hanyar dukkan ta da belt a kai.
"Mai shigar da karar kuma ta fadi ta sami rauni yayinda wanda ake tuhumar ya tunkude ta," inji shi.
KU KARANTA: Buhari ya kalubalanci Obasanjo a kan kashe $16bn a fanin wutan lantarki
Mameh ya ce wanda ake tuhuma ya saba dukan matarsa saboda ta gaza ciyar da shi da samar da sauran bukatunsa.
Mai shigar da karar ya ce wadandan laifukan da ake tuhumar Adebayo dashi sun ci karo da sashi na 170 da 171 na dokar masu laifi na jihar Legas 2015.
Sai dai wanda ake zargin ya ce bai aikata laifukan da aka karanto masa ba.
Alkalin kotun, Mr. B.I. Bakare ya bayar da belin wanda ake zargin a kan kudi N150,000 tare da mutane biyu da suka tsaya masa.
Ya ce masu tsaya masa sai sun kasance masu sana'a kuma su gabatar da shedar biyan haraji ga gwamnatin jihar legas.
Alkalin ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Yuli.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng