Wata gobara ta kone shago 1 da daki 12 a birnin Kano

Wata gobara ta kone shago 1 da daki 12 a birnin Kano

A kalla daki 12 da shago 1 ne wuta ta kone kurmus a wata gobara da ta tashi a layin Mai Unguwa dake unguwar Tudun Murtala a birnin Kano.

Kakakin hukumar kwana-kwana gobara ta jihar Kano, Alhaji Saidu Mohammed, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) jiya, Litinin, a Kano cewar lamarin ya faru ne da misalign 11:50 na safiyar ranar.

Mun samu wani kiran gaggawa daga wani mutum, Malam Abdullahi, da misalign 11:50 na safe inda ya sanar da mu cewar wani gidan dabdalar jama’a na cid a wuta.

Wata gobara ta kone shago 1 da daki 12 a birnin Kano
Wata gobara a birnin Kano

“Ba tare da bata lokaci ba muka aika ma’aikatan mu ya zuwa wurin da misalign 12:15 domin su kasha wutar,” a cewar Mohammed.

Kazalika ya bayyana cewar, har yanzu suna binciken mnusabbabin tashin gobarar.

DUBA WANNAN: Dubi fuskoki da makudan kudin da aka samu a wurin wasu 'yan wala-wala

A wani labarin mai kamanceceniya da wannan, daga Kano, kakakin hukumar kasha gobara ya bayyana cewar wani matashi, Bashir Haruna, mai shekaru 15 ya mutu bayan ya fada wanu rowan kududdufi dake layin Malam Sani Soron Dinki a unguwar Sheka da yammacin ranar Lahadi.

Wani mutum ne ya sanar da hukumar kwana-kwana cewar gawar wani yaro na yawo a kan ruwa da misalign karfe 5:40 na yamma, kamar Mohammed ya bayyana.

Ya kara da cewa jam’ian hukumar kwana-kwana sun isa wurin da misalign karfe 6:10 na yamma inda suka samu yaron ba cikin hayyacin sa ba, saidai kafin a karasa da shi Asibiti ya mutu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel