Hukumar Soji ta fara sayar da filayenta na Bariki don nemawa sojoji wuraren zama
- An sami karin yawan sojoji dake wa Najeriya dawainiya a shekarun nan
- Hukumar Soji tana da kadarar filaye da yawa a fadin kasar nan
- Yawancin sojojin bayan bauta sukan qare a gararamba saboda babu isassun kudin ritaya
Rundunar sojojin najeriya ta fitarda da filin ta da ta yi niyyar gina bariki don saidawa ga jama'a don gina gidajen kansu ko na haya.
Wannan ya zo ne a lokacin da sojojin suke fuskantar matsalar gidajen zama.
A shekaru hudu da suka wuce ne, Daily Trust ta ruwaito yanda aka rabawa manyan sojojin bangare daga cikin filin da aka ware don gina bariki a Asokoro, Abuja.
Bincike ya nuna cewa, filin da ake magana yanzu yana nan a fuloti mai lamba 2302,mai girman hectare 248.19,a Mogadishu cantonment.
Wani binciken ya nuna cewa birnin tarayya ta bada filin ne don magance matsalar rashin gidajen zama da sojojin dake aiki a Abuja suke fuskanta.
Wannan filin dai shugaban sojojin ya mika shi ne ga Nigeria Army Properties Limited (NAPL) don gina gidajen zama na siyarwa.
Kamfanin zai gina gidaje kashi 6 ne da kudin su ya fara da Naira miliyan 11 zuwa Naira miliyan 125 wanda yafi karfin da yawa daga cikin sojojin.
Asokoro Hills Estate, wani bangare na NAPL su suka fara siyarda gidajen,wanda a halin yanzu suna ta talla da raba fom.
DUBA WANNAN: PDP zata iya hadewa da tsofin abokai
A rahoton da Daily Trust ta samu, gida mai dakunan barci 6, ansa mishi kudi Naira miliyan 125, mai dakunan barci 5, Naira miliyan 122.
Bene mai dakunan barci 4, Naira miliyan 81,502,526. Wanda ba Bene ba kuma Naira 50,418,707. Mai dakunan barci 3 kuma Naira miliyan 31,016,380. Mai dakunan barci biyu kuma, Naira miliyan 23,566,131.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng