N-PDP: Ba mu ba Shugaba Buhari wani wa'adi ba - Kawu Baraje

N-PDP: Ba mu ba Shugaba Buhari wani wa'adi ba - Kawu Baraje

‘Daya daga cikin manyan ‘Yan APC a Jihar Kwara kuma Jagoran nPDP Alhaji Kawu Baraje ya bayyana cewa dama can ba su ba Shugaba Buhari wani wa’adi a wasikar da su ka aika masa kwanaki ba.

N-PDP: Ba mu ba Shugaba Buhari wani wa'adi ba - Kawu Baraje
Kawu Baraje yace 'Yan N-PDP su na ganin ta kan su a APC

‘Yan nPDP sun koka da cewa ba a damawa da su a Gwamnatin Buhari duk da cewa da gumin su aka kafa Gwamnati a 2015. Kawu Baraje ya bayyanawa manema labarai a Garin Ilorin cewa shawara ce kurum su ka ba Shugaban kasar.

Alhaji Kawu Baraje ya kuma tabbatar da cewa yau Litinin da rana ne Uwar Jam’iyyar APC mai mulki a kasar za ta zauna da tsofaffin ‘Yan PDP da ke Jam’iyyar. Jam’iyyar APC dai na kokarin ceto Jam’iyyar ne daga rasa jiga-jigan na ta.

KU KARANTA: Ko ‘Yan N-PDP na iya takawa Shugaban kasa Buhari burki a 2019?

Baraje ya koka da rikicin da ya barke a wajen zaben shugabannin Jam’iyyar APC inda a Jihohi 21 aka samu bangarori dabam-dabam na shugabanni. Baraje yace idan ba ayi maza an dinke wannan barakar ba dai kadan ma aka gani a APC.

Babban ‘Dan siyasar yace abin da tsofaffin ‘Yan PDP da ke Jam’iyyar ta APC ke fuskanta yanzu ya fi abin da su ka fuskanta a lokacin su na PDP. ‘Yan nPDP sun hada da Bukola Saraki, Yakubu Dogara, Rabiu Kwankwaso, Aliyu Wammako dsr.

Dama dai kun ji cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewa Shugaba Buhari na bukatar tsofaffin ‘Yan Jam’iyyar PDP da su ka narke cikin tafiyar APC domin ya lashe zabe mai zuwa na 2019 musamman a Jihar sa ta Kwara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng