An sace Iyalin wani rikakken ‘Dan kasuwa a Birnin Gwarin Jihar Kaduna

An sace Iyalin wani rikakken ‘Dan kasuwa a Birnin Gwarin Jihar Kaduna

- ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da matan wani mai kudi a Birnin Gwari

- Sama da ‘Yan bindiga 80 su ka farma Garin na Birnin Gwari cikin dare

- A baya an yi kira Gwamnati ta kafa dokar ta-baci a Yankin Birnin Gwari

Mun samu labari cewa wasu ‘Yan bindiga da ba a san daga inda su ka fito ba sun sace Iyalin wani mutumi a Garin Birnin Gwari. Wannan mutumi mai suna Adamu Nakwana hamshakin ‘Dan kasuwa ne.

Jaridar Daily Trust ta kasar nan ta rahoto cewa a cikin tsakar daren yau ne wasu ‘Yan bindiga sun yi gaba da Matan Alhaji Adamu Nakwana a wani Kauye mai suna Maganda da ke cikin Karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

KU KARANTA: An gano inda 'Yan kwaye ke wanke 10 su tsoma 20

Kamar yadda labari ya zo mana, ‘Yan bindigar sun saki guda daga cikin Matan wannan mutumi inda su ka bada lambar wayar su domin a tuntube su. Wani da abin ya faru a gaban su yace sama da ‘Yan bindiga 80 su ka shigo Birnin Gwari.

‘Yan bindigan dai kai tsaye su ka wuce gidan wannan ‘Dan kasuwa ba tare da taba kowa a Garin ba. Dazu da sassafe dai mu ka ji cewa an tuntubi Jami’an ‘Yan Sandan Jihar amma ba su yi magana game da wannan mummunan abu ba.

Yanzu dai mutanen Gari sun shiga dar-dar inda wadannan ‘Yan bindiga ke jira a tuntube su a waya domin a bada kudi don su saki ragowar Iyalin wannan mutumi. Gwamnati tayi kokarin baza Jamian tsaro a Yankin amma har yanzu ba a tsira ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel