‘Yan sanda sun gano N22m na bogi a jihar Gombe

‘Yan sanda sun gano N22m na bogi a jihar Gombe

- Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya a jihar Gombe sun gano wasu kudade na bogi har kimanin N22m lokacin da suke gudanar da aikin bincike a Gombe

- Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Mr. Shina Olukolu ya bayyana cewa ‘yan kungiyar FSARS ne sukayi nasarar damke wadanda ake zargin da wadannan makudan kudade na bogi a kan hanyar Billiri

- Daya daga cikin wadanda aka kama mai suna Sani Ibrahim, ya bayyana cewa ya shiga harkar buga kudin bogin ne domin biyawa kansa bukatu

Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya a jihar Gombe sun gano wasu kudade na bogi har kimanin N22m lokacin da suke gudanar da aikin bincike a Gombe.

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Mista Shina Olukolu ya bayyana cewa ‘yan kungiyar FSARS ne suka yi nasarar damke wadanda ake zargin da wadannan makudan kudade na bogi a kan hanyar Billiri a yankin jihar Gombe.

‘Yan sanda sun gano N22m na bogi a jihar Gombe
‘Yan sanda sun gano N22m na bogi a jihar Gombe

Daya daga cikin wadanda aka kama mai suna Sani Ibrahim, ya bayyana cewa ya shiga harkar buga kudin bogin ne domin biyawa kansa bukatu, inda yace wani Alhaji ne ya saka shi a harkar a shekarar data gabata lokacin tattalin arzikin Najeriya yayi kasa.

KU KARANTA KUMA: 2019: Akwai makirci da ake shiryawa na doke shugaba Buhari daga kujerarsa - Sanata Marafa

Bayan haka kwamishinan ‘Yan Sandan ya gargadi ‘yan siyasar jihar dasu guji haddasa rikicin siyasa saboda hukumar bazata dauki hakan ba, musamman ga zaben jam’iyyar APC da za’a sake a ranar Asabar, a jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel