Gwamnatin Tarayya ta warewa Jami’ar Nsukka Naira Biliyan 1.3
- Gwamnatin Tarayya ta cika alkawarin da tayi wa Jami’ar Nsukka
- Shugaba Buhari ya aikawa Malaman Makarantar kudi Biliyan 1.3
- Malaman na Jami’a sun yi shekara da shekaru su na sa ran kudin
Mun samu labari cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta saki makudan kudin da su ka haura Biliyan 1 ga Malaman Jami’ar Tarayya ta Nsukka da su ka dade su na jiran tsammani.
Kamar yadda mu ka samu labari daga manema labarai, Dr Ifeanyichukwu Abada wanda shi ne Shugaban Kungiyar ASUU na Malaman Jami’ar Nsukka ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ta saki kudin da aka yi masu alkawari.
Akwai wasu alawus da Gwamnatin Tarayya ta ba Jami’o’in kasar wanda sai yanzu Jami’ar ta Nsukka ta samu rabon ta. Kudin dai sun kai Naira Biliyan 1.3 da Malaman Makarantar ke bin Gwamnatin Tarayya bashi tun shekarar 2009.
KU KARANTA: Gwamnan PDP yayi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari
Shugaban Jami’ar ta UNN Benjamin Ozumba ya bayyana cewa za a biya Malaman Makarantar wannan kudin ne sahu bayan sahu. Malaman Makarantar sun yi matukar farin cikin jin cewa za a saki wadannan kudin ne a makon nan.
Dama dai tun kwanakin baya Gwamnatin Tarayya ta biya Ma’aikatan na Jami’o’i duk kudin da su ka dade su na bin bashi bayan sun tafi wata ‘yar doguwar yajin aiki a fadin kasar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng