Naci dambun kuturu: Saraki ya kara gayyatar Sifeto Idris a karo na uku domin amsa wasu tambayoyi

Naci dambun kuturu: Saraki ya kara gayyatar Sifeto Idris a karo na uku domin amsa wasu tambayoyi

- Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya sake gayyatar Sifeta Janar na Yan sanda da sauran shugabanin hukumomin tsaro

- Saraki ya ce ya zama dole majalisar ta gayyaci shugabanin ne saboda yadda tsaro ke kara tabarbarewa musamman yadda aka sace wasu mutane 87 a jihar Kaduna

- Wannan dai ba shine karo na farko da Majalisar ke gayyatar Sifeta Janar din ba cikin kwanakin nan

Shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki ya sake gayyatar Sifeta Janar na Hukumar Yansandan Najeriya tare da shugabanin hukumar tsaro ta farin hula DSS ta kuma shugaban sojojin Najeriya su bayyana gaban majalisar domin amsa tambayoyi a kan sace wasu mutane da akayi a jihar Kaduna.

Naci dambun kuturu: Saraki ya kara gayyatar Sifeto Idris a karo na uku domin amsa wasu tambayoyi
Naci dambun kuturu: Saraki ya kara gayyatar Sifeto Idris a karo na uku domin amsa wasu tambayoyi

A yau Laraba, Saraki ya yi tsokaci da hanyar amfani da shafinsa na kafar Twitter inda ya ce an sake sace wasu mutane 87 a kan titin kasar nan.

KU KARANTA: Murna ta koma ciki: Gwamnatin tarayya ta umurci kotu ta janye belin Dino Melaye

Shugaban majalisan ya kara da cewa ba za'a zuba idanu ana kallon irin wadandan abubuwa na faruwa ba hakan yasa ya ce shugabanin tsaro na Najeriya su bayyana a zauren majalisar.

Wannan dai ba shine karo na farko da majalisar ke gayyatar Sifeta Janar na 'yan sanda ba duk da cewa a wancan lokutan bai amsa gayyatar da kansa ba, ya dai aike da wakili wanda hakan bai yiwa majalisar dadi ba.

Rashin gurfanar nasa gaban majalisar ya janyo wasu cece-kuce tsakanin majalisar ta dattawa da Sifeta Janar na yan sandan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel