'Yan bindiga sun sace fasinjoji 87 a babban titin zuwa Kaduna
- Wasu yan bindiga sunyi awon gaba da fasinjoji da dama a hanyar jihar Kaduna
- Wani jami'in NURTW ya ce yan bindigan sun tsare sama da motocci 15 ciki har da tankoki, da motoccin haya
- Sojojin Najeriya sun halaka wasu yan bindiga 10 a Adamawa, sun karbe babura 18 da makamai
Rahotanni sa muka samu sunce a kalla fasinjoji 87 ne wasu yan bindiga sunka sace a hanyar Birnin-Gwari da ke jihar Kaduna.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa yan bindigan sun zabi mutanen da suka sace ne bisa yanayin tufafin da suke sanye ta ita kuna suka shige da su cikin daji.
Jami'an Kungiyar direbobi na kasa NURTW ne suka tabbatar da afkuwar lamarin inda suka gargadi mambobin su da su kauracewa bin hanyar har sai jami'an tsaro sun isa wurin don magance yan bindigan.
KU KARANTA: Jihohi 5 da suka fi sauran yawan albarkatun man fetur a Najeriya
Rahotani sun ce mafi yawancin fasinjojin da aka sace mutane ne da ke hanyar su na zuwa kudanci ko arewacin Najeriya.
Wani jami'in NURTW ya ce: "Yan bindigan sun tare sama da motocci guda 15 wanda suka hada da tankoki, bus da wasu motoccin hanya inda suka rika zaban mutanen da zasu sace bisa yanayin tufafin da suke sanye da ita kuma suka shige da su daji.
"Mun gano cewa maso garkuwa da mutanen sun fara tuntunbar iyalan wadanda suka sace inda suke bukatar a biya su miliyoyin naira.
"An kashe wani mutum da wata mace yayin da kuma an sake sace wasu mutane guda hudu.
"Wani jami'in kungiyar mu na NUTRW ya gargade mu da mu kauracewa bin hanyar har sai jami'an tsaro sun je sun magance abin da ke faruwa a hanyar."
A wata labarin kuma, Legit.ng ta kawo muku rahoton ina sojojin da suke atisaye a garin Numan sun halaka yan bindiga guda 10 yayin wani artabu da sukayi da su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng