Hotunan taron lalata dubban bindigogi a jihar Zamfara

Hotunan taron lalata dubban bindigogi a jihar Zamfara

Gwamnatin jihar Zamfara tare da hadin gwuiwar jami’an tsaron Najeriya da kuma wasu kungiyoyin turawa sun yi taron lalata wasu bindigogi masu dumbin yawa.

Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya jagorancin taron lalata makaman. Akwai jami’an tsaro da wakilan kungiyoyi masu zaman kan su, na gida da na waje, da suka halarci taron.

Hotunan taron lalata dubban bindigogi a jihar Zamfara
Taron lalata dubban bindigogi a jihar Zamfara

Hotunan taron lalata dubban bindigogi a jihar Zamfara
Taron lalata dubban bindigogi a jihar Zamfara

Hotunan taron lalata dubban bindigogi a jihar Zamfara
An lalata dubban bindigogi a jihar Zamfara

Jihar Zamafara ta dade tana fama da rigingimu daga ‘yan fashi da makami da kuma ‘yan bindiga. Rigingimun sun yi sanadiyar salwantar rayuka da dama a sassan jihar daban-daban.

DUBA WANNAN: Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram biyu yayin kokarin ceto wani tsoho

An yi tsammanin riginmun jihar zasu lafa bayan kisan wani kasurgin jagoran ‘yan ta’adda a jihar mai suna Buharin Daji. Saidai bata canja zani ba bayan kisan Buharin Daji, domin kuwa ‘yan bindiga sun cigaba da cin Karen su babu babbaka.

A yayin wani jawabi da shugaba Buhari ya yi a kasar Amurka, ya bayyana cewar an kasha mutane a jihar Zamfara fiye da wadanda aka kashe a jihohin Taraba da Benuwe.

Hotunan taron lalata dubban bindigogi a jihar Zamfara
Taron lalata dubban bindigogi a jihar Zamfara

Hotunan taron lalata dubban bindigogi a jihar Zamfara
Dubban bindigogi da aka lalata a jihar Zamfara

Hotunan taron lalata dubban bindigogi a jihar Zamfara
Taron lalata dubban bindigogi a jihar Zamfara

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng