Dakarun sojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram biyu yayin kubutar da wani tsoho

Dakarun sojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram biyu yayin kubutar da wani tsoho

- Wani jarumin sojan Najeriya ya kubutar da wani tsoho daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram

- An yi musayar wuta tsakanin mayakan kungiyar Boko Haram da dakarun soji kafin su kwato tsohon

- Dakarun Soji sun kasha biyu daga cikin mayakan kungiyar ta Boko Haram yayin musayar wuta

Wani jarumin sojan Najeriya ya kubutar da wani tsoho daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram bayan musayar wuta da ‘yan ta’addar.

Jami’in soji, Kanal Onyema Nwachukwu, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fito yau, Litinin, 14 ga watan Mayu.

Lamarin ya faru ne ranar juma’a a kauyen Gobara dake karamar hukumar Gwoza a jihar Borno inda shugaban rundunar soji, bataliya ta 192, Laftanal Asajwun Ahmadu, ya dauko tsohon a kafadar sa.

Dakarun sojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram biyu yayin kubutar da wani tsoho
Dakarun sojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram biyu yayin kubutar da wani tsoho

An kashe mayakan kungiyar Boko Haram biyu yayin musayar wuta da dakarun sojin Najeriya.

DUBA WANNAN: Wata mata ta rasa ran ta bayan tayi allan-baku daga cikin mota ana tsaka da tafiya

Jawabin ya kara da cewar mayakan kungiyar ta Boko Haram sun kama tsohon tare da mayar das hi fursunan yaki. Yanzu haka dakarun soji sun dauki tsohon ya zuwa cibiyar duba lafiyar sojojin bataliya ta 192 domin cigaba da bashi kulawa.

Kazalika dakarun sojin na Ofireshon Lafiya Dole sun yi nasarar kwato wasu makamai daga hannun mayakan da suka kasha tare da lalata maboyar su dake kauyen Gobara da kuma kauyukan Shiyadawe Fulani da Shidawaye Bulama duk a karkashin karamar hukumar Gwoza.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng