Wata mata tayi tsallen burgu ta diro ta tagar mota ana tsaka da tafiya
- Wata mata da ba a tantance ko wacece ba ta daka tsalle ta diro ta tagar mota ana tsaka da tafiya.
- Matar ta diro daga motar ne ranar juma'a a daidai ginin Nestle Water Company dake Abaji a kan titin Abuja zuwa Lokoja
- An bayyana cewar matar da ta mutu 'yar asalin kauyen Gundunkarya ne a jihar Nasarawa, kuma ta kawo doya ne kasuwar Kwali
Wata mata da ba a tantance ko wacece ba ta daka tsalle ta diro ta tagar mota ana tsaka da tafiya.
Matar ta diro daga motar ne ranar juma'a a daidai ginin Nestle Water Company dake Abaji a kan titin Abuja zuwa Lokoja.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:45 na safe bayan tayar motar kirar Golf mai lambar rijista KRV 28 MF ta fita ana tsaka da tafiya.
Ya ce, matar dake zaune a kujerar gaba, ta bude kofar motar ta daka tsalle ta fito, saidai motar ta take ta har lahira bayan dirowar ta.
"Daya daga cikin tayar motar ce ta fice, hakan ya saka direban kasa sarrafa motar, ita kuma matar ta bude kofar motar ta diro amma sai motar ta take ta," a cewar shaidar.
An bayyana cewar matar da ta mutu 'yar asalin kauyen Gundunkarya ne a jihar Nasarawa, kuma ta kawo doya ne kasuwar Kwali.
DUBA WANNAN: APC ta ja kunnen gwamna Rochas, ta kira shi rudadde
Kakakin hukumar kiyaye hadurra a ofishin Abaji, Olasupo Esuruoso, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da dora alhakin a kan gudun wuce kima.
Esuruoso ya ce tuni suka mika gawar matar ga 'yan uwan ta yayin da aka garzaya da direban motar zuwa asibiti domin kulawa da lafiyar sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng