Cakwakiyar aure: ‘Yan sanda sun cafke iyaye da ‘yan uwan wata amarya da taki tarewa gidan ango

Cakwakiyar aure: ‘Yan sanda sun cafke iyaye da ‘yan uwan wata amarya da taki tarewa gidan ango

'Yan sanda akaramar hukumar Suleja dake jihar Neja sun tabbatar da kama iyaye da ‘yan uwan wata amarya da taki tarewa gidan angon ta bayan daurin aure.

‘Yan sanda sun kama iyaye da ‘yan uwan amaryar ne bayan surukin su, Shuaib Dauda, ya shigar da korafi bayan an nemi amarya an rasa sa’i’o kadan da daura aure.

Wani jami’in dan sanda a ofishin su dake Kaduna Road, Aliyu Lawal, ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai.

Mista Lawal ya bayyana cewar lamarin ya faru ne ranar 6 ga watan Mayu da muke ciki, ranar da ango Dauda, mai aikin kanikanci, ya zo ya sanar da su cewar mutanen day a tura domin dauko amarya sun dawo sun sanar das hi cewar basu gan tab a, kuma an neme ta an rasa.

Cakwakiyar aure: ‘Yan sanda sun cafke iyaye da ‘yan uwan wata amarya da taki tarewa gidan ango
Cakwakiyar aure: ‘Yan sanda sun cafke iyaye da ‘yan uwan wata amarya da taki tarewa gidan ango

Dan sandan ya kara da cewa, rashin ganin amarya ya jawo barkewar rikici a unguwar da suke, hakan ya saka hukuma ta kama iyayen amaryar da kuma madaurin auren ta, wato waliyyin ta.

Saidai mahaifin amaryar, Abubakar Haruna da aka fi kira da Zakiru, ya shaidawa ‘yan sanda cewar, ya aurar da ‘ya’ya mata biyu ne a wannan rana kuma kafin auren su saida mazajen da zasu aura suka amince cewar zasu cika dukkan al’adun aure da suka hada da kayayyaki da akwatunan aure, amma bayan daurin aure sai Dauda y ace shi ba zai iya sayen kayan da akwatunan ba klamar yadda aka yi yarjejeniya da shi ba.

DUBA WANNAN:

Ya kara da cewar hakan ne ya saka amaryar ta gudu ta buya a gidan makwabta musamman ganin cewar angon ‘yar uwar ta ya cika alkawarin day a dauka.

Malam Haruna ya bayyana cewar, abokan ango Dauda ne suka tayar da rikici a unguwar saboda absu ga amaryar da suka zo dauka ba.

Yanzu dai amarya Fiddausi ta koma gidan iyayen ta yayin da ango Dauda ke neman a dawo masa da kudi N260,000 da ya kasha a kafin aure.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng