Dalilin da ya sa Mustafa Lamido ya rasa sarautar sa a Jigawa

Dalilin da ya sa Mustafa Lamido ya rasa sarautar sa a Jigawa

Kwanakin baya daya daga cikin ‘Ya ‘yan tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido kuma mai neman Shugaban kasa ya rasa sarautar sa. An tsige Lamido ne daga sarautar sa ta Hakimin Garin Bamaina da ke Karamar Hukumar Birnin Kudu.

Sakataren Masarautar Kasar Dutse Alhaji Ahmed Malami yayi magana da Jaridar Daily Trust inda ya bayyana dalilin da ya sa aka dauki wannan mataki. Malami yace doka ce cewa ba a hada harkar siyasa da kuma sarautar Gari na Hakimi.

Dalilin da ya sa Mustafa Lamido ya rasa sarautar sa a Jigawa
'Dan gidan Sule Lamido zai yi takarar kujerar Sanata

Ahmed Malami yace da zarar mutum yayi niyyar shiga siyasa dole ya ajiye sarautar Gari a gefe guda. Akwai maganar cewa Mustafa Sule Lamido kuwa yana neman takarar kujerar Sanatan Jigawa ta tsakiya a zabe mai zuwa na 2019.

KU KARANTA: Ka ji abin da rashin albashi ya sa wani ya aikata

Sakataren Masarautar yace wannan doka ta dade ana amfani da ita. Kuma dai har yanzu Lamido na rike da rawanin sa na Santurakin Dutse. Wasu na cewa akwai siyasa a lamarin wanda dai Gwamna na yanzu da ke Jam'iyyar APC ya karyata.

Dokar dai ta hau kan Dokajin Dutse Alhaji Aminu Wada Abubakar wanda ya rasa Hakimancin Garin Kiyawa bayan ya nuna sha’awar siyasa inj Sakataren Masarautar Kasar Dusten a Jihar Jigawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng