Da mun biyewa El-Rufai da sai an yi shekaru 40 Kaduna ba ta gama biyan bashi ba – Shehu Sani

Da mun biyewa El-Rufai da sai an yi shekaru 40 Kaduna ba ta gama biyan bashi ba – Shehu Sani

Shugaban kwamitin bashi a Majalisar Dattawa watau Sanata Shehu Sani ya ba Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai shawara yayi amfani da abin da ya samu yayi wa Jihar aiki lokacin da yayi hira da manema labarai kwanan nan.

Sanatan ya bayyana cewa sun ki amincewa da bashin Jihar Kaduna ne saboda kudin da ake bin Jihar sun yi yawa. Yanzu haka dai bashin da ke kan Jihar ya haura Dala Miliyan 220 wanda ya sa ta ke ta biyu a jerin masu tarin bashi.

Da mun biyewa El-Rufai da sai an yi shekaru 40 Kaduna ba ta gama biyan bashi ba – Shehu Sani
Sanata Shehu Sani yace bashin Jihar Kaduna yayi yawa

Sanata Shehu Sani yace kaf ‘Yan Majalisar Dattawan Jihar Kaduna har da na jam’iyyar PDP ba su amince da bashin ba don haka ba rikicin da ke tsakanin su ne ya sa aka hana Jihar bashi ba, ya kuma ce Gwamnan bai tuntube su ba.

Sani yace mai neman bashin banki ai ba zai buge da zagin Ma’aikatan bankin ba inda yace abin da Gwamnan yayi wa Sanatoci kenan. Sani yace dole ayi wa Majalisa bayanin yadda kake neman kashe wannan kudi amma Gwamnan bai yi ba.

KU KARANTA: Sanatan Kaduna ya koka da cewa El-Rufai da Oyegun za su kashe APC

Sanatan na APC yace irin su Jihar Gombe duk da su na aiki ba a taba neman bashi ba don haka yace babu dalilin da zai sa Gwamnan da zai yi shekara 8 ya bar wa Jihar sa bashin da za ayi shekaru 20 ko 30 ko 40 ba a gama biya ba bayan tafiyar sa.

A karshen watan Maris, Majalisar Dattawa ta hana Gwamnatin Jihar Kaduna cin bashi daga bankin Duniya wanda hakan ta sa Gwamnan Jihar Malam Nasir El-Rufai ya tsinewa Sanatocin Jihar ya kuma ce su ne manyan makiyan Jihar Kaduna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel