Kwamandan Peace Corps na kasa ya roki kotu ta dakatar da shari'ar da ake masa
A ranar 11 ga watan Yuni mai zuwa ne wata babban kotun Abuja zata zartas da hukunci a kan wata kara da shugaban hukumar Peace Corp na Najeriya, Mr. Dickson Akoh ya shigar inda ya ke rokon kotu ta dakatar da shari'ar da ake masa.
Lauya mai kare shugaban Peace Corp, John Ochogwu yana son kotu ta dakatar da shari'ar da ake wa wanda yake karewa har sai lokacin da akayi biyaya ga umurnin da wata kotun ta bayar a baya inda ta umurci 'yan sanda su bude hedkwatan Peace Corp da suka rufe a Abuja.
Ochogwu ya ce akwai wasu takardu da ke kulle cikin hedkwatan hukumar ta Peace Corp da ya bukatar gabatar da su a kotu don kare kwamandan na Peace Corps amma hakan ba zai yiwu ba har sai yan sandan sun bude hedkwatan hukumar.
KU KARANTA: An kara kama shi da laifin fashi da makami kwana 25 da sakin sa daga gidan yari
Mr. Akoh wanda ya hallarci zaman shari'ar wanda akayi yau Talata yana fuskantar tuhume-tuhume kan wasu laifuka 13 ne da hukumar yan sanda ta shigar a kansa.
Jami'an tsaro sun kulle hedkwatan Peace Corp da ke Abuja bayan sun cafke kwamandan hukumar da wasu mukarrabansa guda 49 a watan Fabrairun 2017.
Bayan kulle ofishin da yan sanda sukayi, sun garzaya kotu inda suke bukatan kotun ta hallasta matakin da suka dauka amma Alkalin kotun, John Tsoho, ya ki amincewa da hakan inda yace kamata yayi su fara zuwa kotu neman izinin kafin su kulle hedkwatan.
Mr Tsoho ya ce cigaba da garkame hedkwatan na hukumar Peace Corp laifi ne kuma ya bukaci yan sandan su bude hedkwatan amma har yanzu ba su yi biyaya ga wannan umurnin ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng