Mayun karnuka sun cinye yara shida, sun saka jama'a cikin firgici

Mayun karnuka sun cinye yara shida, sun saka jama'a cikin firgici

Wasu mayun karnuka da suka kwace suka bazama cikin wasu kauyuka sun hallaka yara shida a Arewacin kasar Indiya.

'Yan sanda sun ce jama'a sun shiga cikin halin dimuwa sakamakon wannan annoba. Mazauna kauyukan na cigaba da tsare yaran su a gida sannan suna jin tsoron fita gonakin su.

Jami'in 'yan sanda, Anand Kulkarni, ya shaidawa majiyar mu ta wayar tarho cewar yara shida ne karnukan suka kashe a yankin Sitafur dake Uttar Pradesh. Karnukan sun kashe yaran dake tsakanin shekaru biyar zuwa 12 cikin kwanaki goma.

Mayun karnuka sun cinye yara shida, sun saka jama'a cikin firgici
Mayun karnuka sun cinye yara shida, sun saka jama'a cikin firgici

"Karnukan, bakwai zuwa tara, na yawo ne suna neman kananan yara.

Daga watan Nuwamba zuwa yanzu sun kashe a kalla yara 12," a cewar Kulkarni.

DUBA WANNAN: Miji ya kashe matar sa saboda bata dafa masa abinci ba ranar da take farincikin zagayowar ranar haihuwar ta

Karnukan na kai farmaki kan yara a wuraren da babu jama'a musamman gidajen gona ko yayin da yara suka fita bayan gari domin kiwo ko bahaya.

Duk da samun asarar rai sakamakon harin karnuka ba bakon abu bane a kasar Indiya, saidai wannan shine mafi muni da ya taba faruwa a yanki guda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel