‘Yan sanda sun budewa magoya bayan jam’iyyar APC wuta a jihar Ribas – Sanata Magnus Abe
Bisa ga dukkan alamu zaben shugabannin jam’iyyar da aka yi a karshen makon da ya wuce ya bar baya da kura a jihohi da dama dake fadin kasar nan.
A jiya Legit.ng ta sanar da ku cewar wasu jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar APC basu halarci wurin taron zabukan ba a jihohin su yayin da wasu jihohin kuma aka samu barkewar rikici.
Sanata Magnus Abe, Sanata mai wakiltar jihar Ribas ta Kudu maso gabas, ya zargi shugabancin jihar da saba dukkan dokokin zabukan kamar yadda uwar jam’iyya ta gindaya na cewar duk mai sha’awar shiga zabe zai sayi fom din takara sa’o’I 24 kafin a fara gudanar zabe.
Abe ya bayyana cewar kwamitin da aka turo jihar Ribas basu zo a kan kari ba, sannan bayan sun zo sun sanar cewar basu da kayan aiki saboda, a cewar sat un farko, basa son gudanar da zabukan.
DUBA WANNAN: Zabukan shugabannin jam'iyyar APC ya bar baya da kura
Sanata Abe ya ce, “saboda jama’a basu damar sayen fom din takara ba, sai suka dunguma ya zuwa Ofishin jam’iyya domin jiran kwamitin ya karaso su gabatar da korafin sun a rashin samun damar sayen fom amma suna zuwa sai ‘yan sanda suka bude wuta a kan wadannan ‘yan jam’iyya da basu yiwa kowa wata barazana ba.”
Abe na wadannan kalamai ne yayin wata hira da gidan Talabijin na Channels domin jin yadda zaben shugabannin jam’iyyar APC ya kasance.
Jam'iyyar APC a jihar Ribas ta rabu gida biyu, bangare daya na tsohon gwamna kuma ministan sufuri, Amaechi, da bangaren Sanata Abe.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng