2019: Tsohon shugaban kasa Abdulsalam ya bayyana abinda yake bukata daga wurin ‘yan siyasa

2019: Tsohon shugaban kasa Abdulsalam ya bayyana abinda yake bukata daga wurin ‘yan siyasa

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, Janar Abdulsalam Abubakar, ya yi kira ga ‘yan siyasar Najeriya das u zama masu son zaman lafiya yayin da suke takarar neman mukami.

Abdulsalam na wannan kira ne bayan wata ganawar sirri day a yi da wasu ‘yan siyasa daga arewacin Najeriya a jiya, Lahadi. Ya bukaci ,yan siyasar das u saka kishin kasa a sama da bukatun su na siyasa.

Zaman lafiya yana da matukar muhimmanci. Idan babu zaman lafiya, babu kasa, idan babu zaman lafiya babu maganar siyasa. Ya zama wajibi mu hada karfin mu wuri guda domin tabbatar da zaman lafiya a kasar mu,” a kalaman Abdulsalam.

2019: Tsohon shugaban kasa Abdulsalam ya bayyana abinda yake bukata daga wurin ‘yan siyasa
Tsohon shugaban kasa Abdulsalam Abubakar

Alhaji Tanko Yakasai ne ya jagoranci tawagar ‘yan siyasar da suka ziyarci Abdulsalami domin nemawa arewacin Najeriya mafita, kamar yadda ya fada.

DUBA WANNAN: Mata 7 da suka daura damarar kayar da maza a zaben 2019

Kiran Abdulsalam na bukatar ‘yan siyasa su bawa zaman lafiya muhimmanci na zuwa a daidai lokacin da zaben fitar dad an takarar gwamna a jam’iyyar APC ranar Asabar a jihar Ekiti ya karke da rigima.

Kazalika an samu labaran samun rigingimu hard a kisan kai yayin gudanar da zabukan shugabannin mazabu da jam’iyyar APC ta gudanar a fadin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng