Atisayen AYEM AKPATUMA: Duba hotunan aiyukan jin kai da dakarun soji keyi a jihar Taraba
Rundunar sojin Najeriya dake atisayen yaki da aiyukan ta’addanci a jihar Taraba da ake kira AYEM AKPATUMA sun gudanar da wasu aiyukan taimakon al’umma a kananan hukumomin Ibid a Wukari.
A wata sanarwa da mataimakin Darektan yada labarai na hukumar soji, Kanal Kayode Ogunsanya, ya fitar ta bayyan cewar tsohon shugaban rundunar atisayen AYEM AKPATUMA, Birgediya Janar BA Muhammad, ya kai ziyarar gani da ido wata cibiyar ruwa mai amfani da hasken rana da hukumar sojin ke ginawa a karamar hukumar Ibi.
Hukumar sojin ta bayyana cewar da zarar ta kamala aikin cibiyar rowan zata mika ta hannun gwamnatin jihar Taraba. Ana saka ran kamala aikin kafin ranar da za a kamma atisayen, 13 ga watan Mayu, 2018.
DUBA WANNAN:
Kazalika an gudanar da taro da kuma bayar da agaji ga marasa lafiya domin nuna jin dadi da kuma bankwana da mutanen jihar a yayin da atisayen ya zo karshe.
Kimanin mutane 1368 ne suka amfana daga aikin bayar da taimako ga marasa lafiya da hukmar sojin ta gudanar a makarantar ta gabas dake garin Wukari. Mutane da dama dake fama da cututtuka daban-daban sun ci moriyar agajin da aka yi kwanaki biyu ana bayar das hi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng