Cigaba: El-rufai zai gudanar da zabe ta hanyar amfani da na'ura mai kwakwalwa a Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da cewa za'ayi amfani da na'ura mai kwakwalwa da ke amfani da lantarki ne wajen kada kuri'a a zaben kananan hukumomi da za'a gudanar a ranar 12 ga watan Mayu.
Gwamnan jihar Nasir el-Rufai ne ya bayyana hakan a jawabin da yayi a wajen gagamin kaddamar da yakin neman zaben jami'iyyar APC gabanin zaben kananan hukumomin.
Ya ce gwamnatinsa ta kashe mukudden kudaden wajen sayo na'urorin masu amfani da lantarki saboda jam'iyyar APC tana son kuri'un mutane suyi tasiri kuma a dakile magudi.
KU KARANTA: Wasu 'yan tsibbu da suka dade suna damfarar mutane sun shiga hannun hukuma
Wadanda suka hallarci taron kaddamar da yankin neman zaben sun hada da Cif John Oyegun, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Aisha Ahmed, karamar ministan kasfin kudi da tsare-tsare da kuma sauran jiga-jigan jam'iyyar a jihar.
"A duk fadin Najeriya, mune zamu kasance jihar na farko da za ta fara amfani da na'aura mai kwakwalwa wajen kada kuri'a a zabukan kananan hukumomin mu," inji shi.
"Samar da wannan tsarin kada kuri'ar ta hanyar amfani da na'ura mai kwakwalwa, gwamnat tana jadada wa mutane cewa muna da niyyar karfafa demokradiyya kuma za'a kirga kuri'ar kowa."
Gwamnan ya kara da cewa bullowa da na'urar Card reader da INEC tayi a zaben 2015 ya taimaka wajen rage magudin zaben, ita kuma jihar Kaduna ta kara ingantan lamarin da wannan sabon tsarin da ta fito dashi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng