Gaggan barayin mutane tare da yan fashi da makami su 6 sun fada tarkon Yansanda a jihar Katsina

Gaggan barayin mutane tare da yan fashi da makami su 6 sun fada tarkon Yansanda a jihar Katsina

Wani gungun gaggan yan fashi da makami su shidda sun fada komar jami’an Yansanda a jihar Katsina bayan wani musayar wuta da suka yi da jami’an Yansanda a kauyen Kaliyawa-Mahuta, inda aka kwashe tsawon lokaci ana artabu.

Kaakakin rundunar Yansandan jihar, DSP Gambo Isah ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 3 ga watan Mayu, inda yace da misalin karfe 5 na yammacin 17 ga watan Afrilu ne suka samu bayanan sirri game da yan fashin.

KU KARANTA: Gwamnan jihar Kaduna ya karbi bakoncin Babban kwamandan Sojojin runduna ta 1

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakaki Gambo yana fadin sunayen yan fashin kamar haka: Muntari Jibrin, mai shekaru 25, Dabo Hassan 60, Abdullahi Alhaji Samu 20, Tukur Mamman 20, Babangida Saidu 27 da kuma Ishaku Yusuf 20.

Gaggan barayin mutane tare da yan fashi da makami su 6 sun fada tarkon Yansanda a jihar Katsina
Yan fashin

DSP Gambo yace ba tare da bata lokaci ba, nan da nan jami’an Yansanda suka bazama zuwa kauyen, inda suka samu nasarar tarwatsa miyagun mutanen, suka kama shida, sa’annan suka hallaka wasu, inji rahton Daily Trust.

“Mun samu nasarar tarwatsa yan fashin bayan an sha musayar wuta, kuma mun kwato bindiga kirar AK 47, da wasu kananan bindigu, alburusai da dama, kayan Sojoji, wata riga dake dauke da layu da sauran kayayyaki.” Inji shi.

Yan fashin sun tabbatar da miyagun ayyukan da suke aikawata, inda suka amsa laifin kai hare haren fashi da makami da kuma yin garkuwa da mutane akan hanyar Zaria zuwa Kaduna, Funtuwa, Dandume, Sabuwa da wani yanki na jihar Zamfara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel