Sai an yi da gaske a bangaren kiwon lafiya a Najeriya - Osinbajo
- Mataimakin Shugaban kasa Yemu Osibajo ya koka da sha’anin kiwon lafiya
- Farfesan yace Shugaba Jonathan bai yi wa kasa aiki da kudin da aka samu ba
- Osinbajo yace sha’anin kiwon lafiya ya tabarbare dole sai an yi babban gyara
Mun samu labari daga Jaridar The Punch ta kasar nan cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara sukar Gwamnatocin baya musamman Magajin sa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan inda yace bai tabuka komai ba.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace shi yayi sanadiyyar tabarbarewar bangaren kiwon lafiya a kasar. Shugaba Buhari yace daga 2010 har zuwa 2015, Gwamnatin Jonathan ba ta maida hankali game da sha’anin kiwon lafiya ba.
Gwamnatin Buhari tayi wannan magana ne ta bakin Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo a wajen wani taron Likitocin kasar nan na kowace shekara da aka yi jiya a Abuja. Osinbajo yace Jonathan yayi sake bai gyara harkar lafiya ba.
KU KARANTA: Masu goyon bayan Obasanjo sun yi kaca-kaca da Buhari
Yemi Osinbajo yake cewa a lokacin Jonathan an saida gangar danyen mai a kan farashin da ya haura Dala 100 a kowace rana amma ya gaza yin wani hobbasa a bangaren kiwon lafiyan don haka Gwamnatin su sai dai ta gaji tarin matsaloli.
Dazu kun ji cewa Farfesa Yemi Osinbajo yace Gwamnatin Buhari za ta cigaba da yin ram da Barayin Najeriya ana binciken su. Mataimakin Shugaban kasar ya bayyana wannan a cikin Garin Ondo.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng