Yanzu Yanzu: Barayin shanu sun kai hari a wani kauyen Zamfara sun kashe mutane 13

Yanzu Yanzu: Barayin shanu sun kai hari a wani kauyen Zamfara sun kashe mutane 13

- Hukumar ‘Yan Sanda tace mutane 13 ne suka rasa rayukansu sakamakon arangamar da akeyi tsakanin barayin shanu da kuma ‘yan kato da gora a arewacin Najeriya

- Mai magana da yawun ‘Yan Sanda Mohammed Shehu ya bayyana cewa ‘Yan kato da gorar sun fafata tsakaninsu a ranar Talata zuwa Laraba a kauyen Fankashi dake Maru

- ‘Yan ta’addan sun kaiwa kauyen hari wanda hakan ya janyo aka fafata tsakaninsu da ‘yan kato da gorar wadanda ke rike da bindigogi kirar baushe

Hukumar ‘Yan Sanda tace mutane 13 ne suka rasa rayukansu sakamakon arangamar da akeyi tsakanin barayin shanu da kuma ‘yan kato da gora a arewacin Najeriya.

Mai magana da yawun ‘Yan Sanda Mohammed Shehu ya bayyana cewa ‘Yan kato da gorar sun fafata tsakaninsu a ranar Talata zuwa Laraba a kauyen Fankashi dake Maru a jihar ta Zamfara.

Ya kara da cewa “Jami’anmu da aka tura don kwantar da tarzomar sun gano gawarwakin mutane 13 da aka kashe wurin rikicin."

Yanzu Yanzu: Barayin shanu sun kai hari a wani kauyen Zamfara sun kashe mutane 13
Yanzu Yanzu: Barayin shanu sun kai hari a wani kauyen Zamfara sun kashe mutane 13

‘Yan ta’addan sun kaiwa kauyen hari wanda hakan ya janyo aka fafata tsakaninsu da ‘yan kato da gorar wadanda ke rike da bindigogi kirar baushe.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya bayyanawa mutanen Najeriya wani sirrin rayuwarsa cewa baya sauraren waka

Gwamnan jihar ya bayar da umurnin cewa duk wanda aka gani da bindiga a harbe shi a yankin jihar.

A ranar Laraba shugaban hukumar ta ‘Yan Sanda Ibrahim Idris ya bayar da umurnin tura jami’an ‘Yan Sandan 200 zuwa jihar ta Zamfara da Kaduna wadda itama ke fuskantar irin wannan matsalar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel