Matasa biyar a jihar Benuwe sun samu aikin soja kyauta, karanta bajintar da suka yi
Shugaban sojin kasar nan, Lt. Janar Tukur Buratai, ya bukaci al'ummar kauyen Gbajimba dake karamar hukumar Guma a jihar Benue da su kawo matasa guda biyar domin daukar su aikin soja kai tsaye.
Kamfanin dillanci labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar Buratai ya yi wannan sanarwa ne a wata ziyara da ya kai ga dakarun soji da aka jibge a yankin don magance hare-hare da yankin ke fama da shi daga makiyaya.

Janar Tukur Buratai, ya bayar da umarci nan take ga kwamandan runduna ta 72, kanal Suleiman Mohammed, wanda yayo masa rakiya domin a tabbatar da an zabo zaratan samari guda biyar a kuma tantance su.
DUBA WANNAN: Abinda nake bukata a wurin ‘yan jaridar Najeriya – Shugaba Buhari
"Dole ne a yau Laraba din nan a tabbatar da an tantance matasan a kuma tura su defot din soji dake Zaria, Alhamis mai zuwa ya zamo suna cikin wadanda suka yi nasara shiga horon aikin soja"
Kamfanin dillacin labarai na Nigeria yace, yankin na Gbajimba na daya daga cikin yankunan da suka fi fama da rikicin makiyaya, lamarin da yayi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyi da dama
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng