Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Jigawa a ranar 7 ga watan Mayu

Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Jigawa a ranar 7 ga watan Mayu

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito a ranar yau Talata, da zarar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga kasar Amurka, ana kuma sa ran zai kai ziyarar yini guda zuwa jihar Jigawa dake yankin Arewa ta tsakiya a kasar nan.

Gwamnan jihar Muhammad Badaru, shine ya bayar da wannan sanarwa yayin ganawa da manema labarai a birnin Dutse da cewar shugaban kasar zai kawo ziyara jihar sa ne domin kaddamar da wasu aikace-aikace.

Badaru ya bayyana cewa, gwamnatin jihar sa tuni ta kammala shirye-shirye na karamci gami da lale maraba da za ta yiwa shugaba Buhari yayin ziyarar sa.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa, babban bakon da ake sa ran ziyarar shi zai kaddamar da wasu sabbin aikace-aikace na hanyoyi da kuma na ruwa a ciki da wajen birnin jihar ta Jigawa.

Gwamna Badaru tare da shugaba Buhari a fadar Villa
Gwamna Badaru tare da shugaba Buhari a fadar Villa

Ya ci gaba da cewa, shugaban kasar zai kuma kaddamar gudanarwar kwamitin zumunta na jihar da a kwana-kwanan nan doka ta kafa shi.

KARANTA KUMA: Wata Daliba dauke da Juna Biyu ta kashe Kanta a jihar Ribas

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan sabuwar doka ta kayyade cewa gwamnatin jihar za ta bayar da tukwicin kudade a kowane wata da zasu tallafa wajen habakar gine-gine a ma'aikatun lafiya, ilimi da sauransu.

Gwamnan ya kara da cewa, shugaba Buhari zai kuma kaddamar da wasu sabbin aikace-aikace na kamfanin madara da nono a karamar hukumar Birnin Kudu da kuma wasu ma'aikatun kiwon lafiya 80 a fadin jihar.

A yayin haka kuma gwamna Badaru yake neman al'ummar jihar da su tabbatar da karramci da nuna kara ta hanyar maraba managarciya yayin ziyarar shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel