Majalisar dattijai ta zabtare kudin fom din takara, duba sabon farashin kowacce kujera
- Majalisar dattijai ta zartar da gyaran sashe mai lamba 6 2010 na kundin dokokin zabe
- Idan dokar ta samu wucewa, zata takawa jam'iyyu birki a kan yadda suke yanke kudin fom din takara
- Shugaba Buhari ya sayi fom din takarar shugaban kasa a kan miliyan N25m a shekarar 2015
Majalisar dattijai ta mayar da kudin fom din takarar shugaban kasa zuwa miliyan N10m.
Ragin kudin na cikin gyaran sashe mai lamba 6 2010 na kundin tsarin dokokin zabe da majalisar ta fara gyarawa tun 30 ga watan Maris.
Idan shugaba Buhari ya saka hannu a kan sabuwar dokar, zata takawa jam'iyyu birki a kan batun yanke kudin fom din takara.
A shekarar 2015, shugaba Buhari, ya sayi fom din takarar shugaban kasa a kan miliyan N25m.
Ga jerin sabon farashin fom din takara kamar yadda majalisar dattijai ta yanke
1. Kansila - N150,000
2. Shugaban karamar hukuma - N250,000
3. Majalisar jiha - N500,000
DUBA WANNAN: Sanata Shehu Sani ya mika kan sa ga hukumar 'yan sanda bisa zargin kisa
4. Majalisar wakilai - Miliyan N1,000,000
5. Majasilar dattijai - Miliyan N2,000,000
6. Gwamna - Miliyan N5,000,000
7. Shugaban kasa - Miliyan N10m
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng