Tsaurin ido: Wata budurwa ta shararawa dan sanda mari, idon ta ya raina fata
A yau, Litinin, hukumar 'yan sanda ta gurfanar da wata mata gaban wata kotun Abuja bisa tuhumar ta da laifin marin dan sanda tare da yi masa barazana.
An gurfanar da matar, Faith Michael; mai shekaru 27, gaban kotu bisa wasu caji guda shida da suka hada da, cin zarafi, hana hukuma aikin ta, da bata suna, laifukan da ta musanta aikatawa.
Dan sanda mai gabatar da kara, Vincent Osuji, ya ce wani mutum ne ya kawo rahoton abinda matar ta yiwa dan sandan ranar 15 ga watan Afrilu.
Dan sandan da aka mara ya sanar da kotu cewar, matar tare da wani mutum sun ci zarafin sa yayin da yake bakin aikin sa a kwanar CBN dake Karu a Abuja.
Ya kara da cewar ya tsayar da wani dan Achaba ne da ya dauko matar amma maimakon ta barshi ya yi aikin sa sai ta fara zakalkale masa kafin daga bisani ta kira wani mutum da suka taru suka ci masa mutunci tare da yi masa barazanar zasu tube masa kayan sa na aiki.
DUBA WANNAN: Za a dauki ma'aikata a hukumar kula da gidajen yari ta kasa, duba karin bayani
Yanzu dai mutumin da ya taimakawa matar wajen cin mutuncin dan sandan ya gudu.
Alkalin kotun, Hassan Ishaq, ya bayar da belin matar a kan N20,000 tare da wanda zai tsaya mata sannan ya daga sauraron karar zuwa ranar 18 ga watan Mayu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng