Yanzu-yanzu: Sakamakon daukan aiki a hukumar fursuna ta kasa ya fito, duba don samun karin bayani
A yau, Litinin, hukumar kula gidajen yari ta kasa (NPS) ta buga sanarwar zata dauki ma'aikata a wasu jaridun kasar nan.
Sanarwar ta bayyana cewar, hukumar NPS na sanar da dukkan 'yan Najeriya dake bukatar aiki da hukumar cewar zasu iya neman aiki da ya dace da takardun su na karatu.
Masu shaidar karatun Digiri, Babbar Diploma, Karamar Difloma, da wadanda suka mallaki takardar kammala karatun sakandire zasu iya neman aiki a hukumar.
Hanyar da za a bi domin neman aikin:
1. Za cike komai ta yanar gizo ne
2. Masu sha'awa zasu ziyarci shafin hukumar a kan www.prisons.gov.ng
3. Duk wanda ya cike fiye da sau daya ya rasa dukkan ragowar
DUBA WANNAN: Jiga-jigan jam'iyyar APC sun kauracewa yiwa shugaba Buhari yakin neman zabe
Sharudan da ake bukatar mai neman aikin ya cika:
1. Ya kasance haifaffen Najeriya
2. Dole ka mallaki daya daga cikin shaidun karatun da aka ambata
3. Ya kasance mutum yana da sakamakon koshin kafiya daga asibitin gwamnati
4. Mutum ya kasance mai halin kirki kuma ba a taba gurfanar da shi gaban kotu ba
5. Idan mutum yana tu'ammali da miyagun kwayoyi ko yana cikin kungiyar tsafi, kada ya nemi aikin
6. Masu shekarun haihuwa 18 zuwa 30 kawai ake bukata
7. Ana bukatar tsawon mutum ya kasance a kalla mita 1.65m ga maza da mita 1.60m ga mata
8. Ilimin na'ura mai kwakwalwa nada matukar mahimmanci
Sanarwar, kamar yadda sakataren hukumar ya sakawa hannu, ta ce za a rufe shafin neman aikin bayan sati shida daga yau.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng