Toh fah: Majalisar Wakilai zata bada sammacin a kamo mata wasu mukarraban shugaba Buhari
- Majalisar Wakilai ta bukaci mambobin kwamiti na musamman don binciken fadar shugaban kasa (SPIP)
- Dan majalisa, Ahman Pategi yace rashin amsa gayyatar da mambobin kwamitin sukayi cin fuska ne ga majalisar
Majalisar Wakilai tayi barazanar bayar da sammaci don kamo mambobin kwamiti na musamman don binciken fadar shugaban kasa 'Special Presidential Investtigation Panel (SPIP) indan har basu bayyana gaban majalisar ba a ranar 8 ga watan Mayu.
Kwamitin majalisar wakilai da ke bincike a kan hallascin kafa kwamitin fadar shugaban kasar ne sukayi wannan barazanar a ranar Alhamis, 26 ga watan Afrilu, bayan Ciyaman din kwamitin yace mambobin SPIP din sunki amsa gayyatar majalisa kamar yadda Daily Times ta ruwaito.
KU KARANTA: Akwai masu daukan nauyin makiyaya masu kai hari a Binuwai - Sojin Najeriya
Shugaban kwamitin majalisar wakilan, Ahman Pategi, yace rashin amsa kirar da mambobin SPIP din sukayi duk da cewa an aika musu gayyata a lokuta da yawa cin fuska ne ga Majalisar Wakilan.
A yayin da yake gabatar da kudirin aika sammaci ga mambobin SPIP din, dan majalisa, Toby Okechukwu yace kundin tsarin mulkin kasa ne ya dora wa majalisar alhakin sa ido a kan yadda fadar shugaban kasar ke gudanar da ayyukan ta.
A wata rahoton a baya, Legit.ng ta ruwaito muku a jiya 26 ga watan Afrilu wasu mambobin majalisar dattawa sun gabatar da kudirin tsige shugaba Muhammadu Buhari saboda tuhumar sa da cire $486 miliyan don sayo jiragen sama kirar Tucano.
Sai dai kudirin nasa na tsige shugaban kasan baiyi tasiri ba bayan Shugaban Majalisa, Bukola Saraki da Sanata Ibn Na'allah sun sanya baki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng