Ashe babu wani aiki da shugaba Buhari ya kaddamar a Bauchi, sai shawagi

Ashe babu wani aiki da shugaba Buhari ya kaddamar a Bauchi, sai shawagi

- A bisa al'ada, sai za'a kaddamar da manyan ayyuka shugaba ke kai ziyara

- Ashe kawai zagayen farkar da masoya shugaban yayi a yau

- Jam'iyyar People's Democratic Party, PDP ta jihar Bauchi, I ta bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari bashi da wani abu da zai gabatar a jihar Bauchin

Ashe babu wani aiki da shugaba Buhari ya kaddamar a Bahuchi, sai shawagi
Ashe babu wani aiki da shugaba Buhari ya kaddamar a Bahuchi, sai shawagi

A cewar babbar jam'iyyar adawa ta PDD, shugaba Buhari babu wani aikin tarayya da ya kawo wa talakawan Bauchi da har ya saka ya baro birnin tarayya, saboda ayyukan da aka yi a jihar basu da ce har sai shugaban kasar ya zo ba.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun gano wasu makamai masu hadari a wani gari dake iyaka da jihar Kebbi

Da yake magana da manema labarai a ranar Larabar nan, Sakataren Jam'iyyar na jiha, Yayanuwa Zainabari, yace bai kamata gwamnan jihar ya gayyato shugaban kasa yazo Bauchi ba kawai dan zai raba Tractors.

A cewar sa, yanzu shekaru uku kenan amma har yau babu wani kwakkwaran abu da gwamnatin jihar ta gabatar wanda zai amfani al'umma. Ya ce, dalilin zuwan shugaban kasar ne yasa gwamnatin jihar ta gyara hanyoyi, sannan tayi wa ko ina ado, kamar dai yanda ake yi ranar sallah.

"Abun kunya ne ace yau shekaru uku babu wani kwakkwaran abu da gwamnatin jihar nan tayi sai yanzu ta samo tractors zata rabawa manoma. A tunani na karamar hukuma ce take da alhakin sayen kayan aikin gona ba gwamnatin jiha ba."

A karshe jam'iyyar ta PDP tayi lale da zuwan shugaban kasar, sannan tayi mashi fatan ban gajiya, sannan kuma tayi addu'ar Allah ya maida shi gida lafiya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng