‘Yar baiwa: An samu wata ta kammala Jami’a da maki 4.97 cikin 5.00 a B.U.K

‘Yar baiwa: An samu wata ta kammala Jami’a da maki 4.97 cikin 5.00 a B.U.K

- Mata sun ciri tuta wajen karatun Boko a Jami’ar Bayero ta Kano

- Kwanan aka yaye ‘Dalibai masu Digirin farko fiye da 5000 a BUK

- Wanda ta ciri tuta a kaf Jami’ar mace ce kuma ta fadi lakanin ta

Kwanan nan ne Jami’ar Bayero da ke Jihar Kano ta yaye ‘Dalibai sama da 8000 na kakar karatun shekarar 2017 da 2018. Daga ciki an samu wasu zakukuran gaske da mafi yawa mata ne da su ka ciri tuta a shekarar nan.

‘Yar baiwa: An samu wata ta kammala Jami’a da maki 4.97 cikin 5.00 a B.U.K
Wata ta gama Jami'ar BUK da makin da babu irin sa

Daga cikin ‘Daliban da aka yaye a bana an samu 72 da su ka fita da kololuwar mataki na farko watau First Class. A cikin wadannan 72 da su ka ciri tuta kuma wata Baiwar Allah ce duk ta sha gaban su a shekarar nan.

Kamar yadda labari ya zo mana daga Jaridar Daily Trust, Rahama Habibu Rabi’u ce ta ciri tuta a kaf Jami’ar Bayero inda ta fita da maki 4.97 cikin 5.00. Rahama ta karanta ilmin rayukan tsirrai ne a tsangayar fasaha.

KU KARANTA: Ya dauki danyen hukunci saboda rashin biya masa bukata

Yanzu dai yara mata su ma sun fara shigowa gari a harkar ilmin zamani. Rahama ta fadawa Jaridar Daily Trust cewa addu’a babu inda ba ta kai ‘diya mace. Rahama tace babu inda ta sha wahala kamar a ajin karshe.

Kwanaki Legit.ng ta rahoto maku cewa NNPC ta dauki nauyin wani Dalibi da ya kammala Digiri da maki 4.93 cikin 5.00 a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Sunan wannan yaro Al-Ameen Bugaje.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng