Jerin jihohi 10 da gwamnatin tarayya zata gina sabbin kamfanonin sarrafa shinkafa

Jerin jihohi 10 da gwamnatin tarayya zata gina sabbin kamfanonin sarrafa shinkafa

A zaman da majalisar zartarwar ta yi yau Laraba, ta amince da kafa manyan masana'antun sarrafa shinkafa guda goma a fadin kasar nan.

Karamin mimistan noma Heineken Lokpobiri ne ya bayyana haka jim kadan da fitowa daga taron da ya gudana a dakin taron dake fadar shugaban kasa dake Abuja.

Mr Lokpobiri ya ce, Nigeria na bukatar masana'antar sarrafa shinkafa sama da 100, maimakon kwaya 21 da kasar nan ke da su.

Jerin jihohi 10 da gwamnatin tarayya zata gina sabbin kamfanonin sarrafa shinkafa
kamfanin sarrafa shinkafa

"A dabarar da gwamnatin tarayya fito da ita shine na yanke shawarar sahale gina karin sabbin masana'antun sarrafa shinkafa guda 100 da kudin su bai gaza bilyan 10.7 ba."

DUBA WANNAN: Kasar Saudiyya ta bayar da gagarumar kyauta ga dan kwallon kafa Mohammed Salah

Ya ce, za'a gina masana'antun ne a jahohin daban daban dake sassan kasar nan. Mr Lokpobiri ya ce, jahohin da za'a gina sune: Bauchi, Kebbi, Anambra, Benue, Zamfara Kogi, Bayelsa, Ogun, Kaduna, Niger.

"Adadin abinda za su rinka samarwa kullum ya kai ton 100." A cewar shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng