Har ila yau: Wani dan majalisar wakilai ya kara ficewa daga jam’iyyar PDP
- A karo na farko wani mamba a majalisar wakilai ya canja sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar SDP
- Dan majalisar, Olamide Oni, mai wakiltar Ijero/Ekiti ta yamma/Efo ya bayyana ficewar sa daga PDP yayin zaman majalisar nay au
- Ya ce ya bar jam’iyyar ne saboda rabuwar kai dake PDP duk da cewar a karkashin inuwar ta ya lashe zaben day a kwo shi majalisar
A karo na farko wani mamba a majalisar wakilai, Olamide Oni, ya canja sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar SDP.
Dan majalisar, Olamide Oni, mai wakiltar Ijero/Ekiti ta yamma/Efo , dake jihar Ekiti ya bayyana ficewar sa daga PDP yayin zaman majalisar na yau, Laraba.
Da yake bayyana dalilin san a ficewa daga PDP, Oni, ya ce rabuwar kai dake jam’iyyar ne sababin barin ta duk da cewar a karkashin inuwar ta ya lashe zaben da ya kwo shi majalisar ta wakilai.
Mista Oni ne dan majalisa na farko day a bayyana shiga jam’iyyar SDP da yanzu ke kokarin hada kan tsofin shugabannin Najeriya da ‘yan Najeriya karkashin jagorancin Obasanjo domin karbar mulki daga hannun jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.
DUBA WANNAN: Bayan sace sandar ikon majalisa ‘yan mazabar sanata Omo-Agege sun yi wata barazana
SDP ta bayyana cewar wasu gwamnoni da mambobin majalisar tarayya daga jam’iyyar APC da PDP zasu shiga jam’iyyar.
Tuni jagororin jam’iyyar PDP; Farfesa Jerry Gana da Tunde Adeniran, suka saka kafa suka fice daga PDP tare da komawa SDP bayan kamala zaben shugabannin jam’iyya a PDP.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng