Jerin jihohin Najeriya 23 da matasa zasu ci moriyar tallafin biliyan N8.6bn na bankin duniya
Nan bada dadewa ba Bankin duniya, a karkashin shirin FADAMA III, zai bayar da tallafin biliyan 8.6bn ga matasa 5,916 da suka kamma karatu basu samu aiki ba dake fadin kasar nan.
Shugaban shirin tallafawa matasan, Kwaji Daguru, ya sanar da haka yayi wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a yau, Talata.
Daguru ya bayyana cewar shirin zai tallafawa matasa 5,916 daga jihohi 23 dake fadin kasar nan.
Jihohin da zasu ci moriyar shirin sune; Abiya, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benuwe, Ebonyi, Ekiti, Jigawa, Katsina, Kebbi, Kogi, Neja, Ogun da Ondo.
Ragowar jihohin sune; Osun, Oyo, Filato, Sokoto, Taraba, Taraba, da kuma birnin tarayya, Abuja.
DUBA WANNAN: Bayan ganawar sirri da Buhari, Alkalin alkalan Najeriya ya ce alkalai basu da laifi
Za a bawa matasan tallafin ne domin su shiga harkar noma gadan-gadan.
Daguru ya ce kudin nan nan a ajiye, raba su kawai za a yi.
"Daga kowanne lokaci zamu iya fara raba kudin musamman ga matasan da zasu yi noman damina," a cewar Daguru.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng