Malaria: Zazzabin cizon sauro da ya gagari jama'a da gwamnatin Najeriya

Malaria: Zazzabin cizon sauro da ya gagari jama'a da gwamnatin Najeriya

- Dalilin da yasa Najeriya bazata iya yakar cutar da take barazana ga kashi 97 a cikin dari na mutanenta.

- Cutar zazzabin cizon sauro ta kasance cutar da ke barazana ga rayuka a kasashe 97 na Tropic

- Babu dabbar da ta kai sauro illa ga mutum a duniya a tarihi

Malaria: Zazzabin cizon sauro da ya gagari jama'a da gwamnatin Najeriya
Malaria: Zazzabin cizon sauro da ya gagari jama'a da gwamnatin Najeriya

A duniya, ana samun kusan miliyan 214 da cutar duk shekara da kuma biliyan 3.3 a kasashe 106 da ke da damar samu. Kusan mutuwar mutane 438,000 aka danganta d cutar a 2015 a Afirika, inda kusan kashi 90 na mace mace daga cutar ne.

Cutar zazzabin cizon sauro wata annoba ce da ta halaka jarirai 400,000 kuma tae halaka mata masu juna biyu a Najeriya.

Masani akan lafiya Ladipo Olabode Taiwo yace gwamnatin tarayya bata kokartawa gurin yaki da cutar.

"Babu takamaiman yawan mutane da gwanatin tarayya ta taimaka don yaki da cutar a kasar."

Ya cigaba da cewa jihohin da basa karkashin PMI don yaki da cutar Global Fund ce ta dau nauyin su.

DUBA WANNAN: An gama BBNAIJA, an wawashe samarin kasar nan kaf

Yayi magana akan rashin kokarin da gwanatin tarayya take yi ta bangaren lafiya.

"Ba don taimakon PMI, global fund da kuma kungiyoyin taimakon kai da kai wadanda ke tallafawa a bangaren lafiya ba da babu wani abin azo a gani da gwanatin tarayya keyi.

"Ranar cutar cizon sauro ta duniya, rana ce ta wayarwa da ilimantar da 'yan kasa akan cutar. Ta yanda masu cutar zasu warke, marasa ita zasu kare kansu sannan kowa zai iya yakar ta." Mista Taiwo ya kara.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng