Sauki ya zo: Masu satar mutane da barayin shanu 1,150 sun saduda a jihar Kaduna
Wasu gungun 'yan ta'adda da yawan su ya kai 1,150 sun yi rantsuwa tare da cin al washin ba zasu kara aikata miyagun laifuka ba a kauyen Anchau dake jihar Kaduna.
'Yan ta'addar da suka tuban sun hada da barayin shanu da masu garkuwa da mutane da kuma 'yan tamore.
Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Kaduna, ASP Mukhtar Aliyu, ya tabbatar da hakan a jiya tare da bayyana cewar 'yan ta'addan sun tuba biyo bayan tattaunawa mai zurfi da hukuma da kuma shugabannin al'umma.
Aliyu ya kara da cewar wannan nasara ne saboda dagewar kwamishinan 'yan sanda a jihar, Austin Iwar, a kan saka shugabannin al'umma da farar hula cikin harkar tsaro.
A nasa bangaren, hakimin karamar hukumar Kubau, Malam Audu Sallau, ya ce an samu wannan nasara ne saboda hadin kan da suke samu daga bangaren jami'an 'yan sanda a jihar.
Sallau ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Kaduna da su basu gudunmawar da suke bukata domin samun zaman lafiya mai dorewa a jihar da ma kasa baki daya.
DUBA WANNAN: Wasu tsageru a jihar Ribas sun takali sojoji, an yi barin wuta da asarar rayuka
"Babu wanda aka yiwa tilas cikin wadanda ta'adda da suka tuba, da kan su suka gamsu da su daina aikata laifuka tare da yin bankwana da aiyukan ta'addanci," a cewar Sallau.
70 daga cikin 'yan ta'addar sun yi rantsuwa da Qur'ani na zasu kara aikata miyagun laifuka ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng