Tabbas Kwankwaso ya kawo ci gaban gine - gine a jihar Kano - Ganduje
Rahotanni da sanadin jaridar Daily Trust sun bayyana cewa, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya yabawa tsohuwar gwamnatin jihar sa karkashin jagorancin Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso da cewar ko shakka ba bu ta kawo ci gaba a cikin jihar.
Ganduje ya yi wannan furuci ne a yayin amsa tambayoyin 'yan jarida a karshe makon da ya gabata dangane da takaddama kan batun zaben kananan hukumomi na jihar, kantar bashi da ta yiwa jihar katutu da kuma wasu ababe da suka shafi jihar.
A yayin amsa tambayoyin 'yan jarida, Ganduje ya bayyana cewa ko shakka babu tsohuwar gwamnatin Kwankwaso ta kawo muhimman ci gaba da kuma habaka ta fuskar gine-gine.
Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnan ya yiwa wannan fashin baki yayin amsa tambayoyi dangane da gine-ginen gidaje da tsohuwar gwamnatin jihar ta kaddamar a wasu sassa dake iyaka da birnin jihar.
Sai dai Ganduje ya ce gwamnatin sa ba za ta iya ci gaba da gudanar da wannan aiki ba sakamakon tsadar kayan aiki da kuma sauyin yanayi na tattalin arziki a kasar nan baki daya.
KARANTA KUMA: Shehi Ɗahiru Bauchi ya nemi Gwamnatin tarayya akan ta saukaka wahalar Talaka a Najeriya
A karshen makon da ya gabata jaridar ta kuma ruwaito cewa, gwamnan ya bayyana ainihin bashin dake kan jihar ta Kano, inda ya bayyana adadin kudi na N300b da tsohuwar gwamnatin Kwankwaso ta bari.
Rahotanni sun bayyana cewa, Ganduje ya kalubalanci duk wani mai takaddama kan batun sakamakon zaben kananan hukumomi na jihar akan ya shigar da kara kotu matukar yana da hujjoji na kare kai.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng