Maganganun shirmen gwamna El-Rufa’i zai kara saukakawa PDP nasarar zabe a shekarar 2019 - Sani Bello

Maganganun shirmen gwamna El-Rufa’i zai kara saukakawa PDP nasarar zabe a shekarar 2019 - Sani Bello

- Dr Muhammad Sani Bello wanda yana daya daga cikin jagororin jam’iyyar PDP yace shirmen da Nasir El-Rufa’I yakeyi yana kara saukakawa PDP cin zabe a shekarar 2019

- Sani Bello yace gwamnatin APC a jihar Kaduna a karkashin shugabancin Nasir El-Rufa’I na nunawa mutanen jihar wariya kuma ta kasa basu kwarin gwiwa akanta

- Dan takarar gwamna a jihar Kaduna karkashin jam’iyyar PDP yayi ikirarin cewa gwamantin ta kasa a fannin ayyukanta na bayar da tsaro ga mutanen jihar

Dr Muhammad Sani Bello wanda yana daya daga cikin jagororin jam’iyyar PDP yace shirmen da Nasir El-Rufa’I yakeyi yana kara saukakawa PDP cin zabe a shekarar 2019.

NAN ta ruwaito cewa Sani Bello yace gwamnatin APC a jihar Kaduna a karkashin shugabancin Nasir El-Rufa’I na nunawa mutanen jihar wariya kuma ta kasa basu kwarin gwiwa akanta.

Dan takarar gwamna a jihar Kaduna karkashin jam’iyyar PDP yayi ikirarin cewa gwamantin ta kasa a fannin ayyukanta na bayar da tsaro ga mutanen jihar.

Maganganun shirmen gwamna El-Rufa’i zai kara saukakawa PDP nasarar zabe a shekarar 2019 - Sani Bello
Maganganun shirmen gwamna El-Rufa’i zai kara saukakawa PDP nasarar zabe a shekarar 2019 - Sani Bello

Sani Bello wanda shine Mainan Zazzau ya kara zargar gwamnatin akan korar malaman makarantar Primary 22,000 datayi, tana cewa ba’a bi ka’idar data kamata ba wurin daukarsu aikin.

Yace kuma mutane 11,000 da aka dauka su maye guraben malan da aka kora aiki basu da horon daya kamata na koyarwa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jami’an ‘Yan Sanda rike da makamai sun mamaye gidan Dino Melaye na birnin tarayya

Idan dai bazaku manta ba a watannin baya ne gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya sallami wasu daga cikin malaman makaranta a jihar bisa zargin cewa sun fadi wani gwaji da yayi masu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng