Zan koma makaranta amma fa idan Buratai ne zai zama maigadin mu - Dalibar Sakandiren Dapchi
- Wata dalibar makarantar Dapchi na Jihar Yobe, inda Boko Haram ta kai hari, ta gindaya sharadin da zai sa ta koma makarantar
- Ta ce za ta koma ne idan har Babban Hafsan Sojin Najeriya, Tukur Burutai, zai gadin makarantar
- Idan kuwa ba haka ba, ta gwammace ta yi ta karatun ta gida
Harin da Boko Haram ta kai Kwalejin Gwamnati na Kimiyya na Mata a Dapchi na Jihar Yobe, ya haifar da cikas wurin zaman dalibai a makarantar. Harin kuma ya haifar da firgici a Jihar wanda cikin shekaru 7, hare-haren da Jihar ta fuskanta ba su da yawa.
Wata dalibar makarantar mai suna Fa'iza Mohammed ta ce ba za ta koma makarantar ba sai dai fa idan Babban Hafsan Sojin Najeriya, Yusuf Tukur Burutai, shi ne mai gadin makarantar.
DUBA WANNAN: Cuwa-cuwan kudi na N13.6bn: Kotu ta dage shari'ar Dasuki zuwa 22 ga watan Maris
Ta bayyana irin bakar wahalar da su ka sha don neman kubuta daga zalunci da rashin imani na Boko Haram. Ta kuma yabawa malaman makarantar bisa kokarin su na ganin sun ba wa daliban kariya.
Fa'iza ta ce madadin rashin yuwuwar Burutai zama mai gadin makarantar, ta na bukatar Gwamnati ta samarwa makarantar cikakkiyar tsaro. Ta kuma ce idan har ba a samar da tsaro ba to ta gwammace ta yi ta karatun ta a gida.
Akwai daliban da har yanzun ba a gan su ba. Iyayen su sun shiga wani hali sun kuma nemi bahasi daga Gwamnatin Jihar. Tuni dai Gwamnatin Jihar ta rufe makarantar na mako 1. Rundunar Sojin Kafa kuma sun tsunduma wurin neman daliban da su ka bace.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng