Ganduje ya nada Attahiru Jega Shugaban cibiyar siyasa ta Kano

Ganduje ya nada Attahiru Jega Shugaban cibiyar siyasa ta Kano

- Gwamnan Kano Ganduje ya ba Attahiru Jega wani babban mukami

- Jega zai shugabanci wata tsangaya da aka kafa domin harkar siyasa

- An dai kafa cibiyar ne domin tunawa da Marigayi ‘Dan Masanin Kano

Dazu nan mu ka samu labari cewa Gwamnatin Jihar Kano ta ba tsohon Shugaban Hukuamr zabe na kasa na INEC watau Attahiru Jega mukami a wata tsangayar siyasa da shugabanci da ke Jihar.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya nada Farfesa Attahiru Jega wannan kujera ne saboda gudumuwar da yayi a fagen siyasar kasar. Gwamnan yayi haka ne domin a karrama Marigayi ‘Dan Masanin Kano Alhaji Maitama Sule da ya rasu kwanaki.

Ganduje ya nada Attahiru Jega Shugaban cibiyar siyasa ta Kano
Gwamnatin Ganduje ta ba Attahiru Jega wani aiki

Gwamnatin Kano ta duba ta ga cewa babu wanda ya dace da rike wannan cibiya sai tsohon Shugaban Hukumar zabe kuma tsohon Shugaban Jami’ar Bayero ta Jihar. Akwai kuma wasu da za su taimaka wajen jagorantar wannan cibiya.

KU KARANTA: Ganduje ya bayyana ainihin bashin da Kwankwaso ya bar masa

Daga cikin ‘Yan kwamitin da aka kafa su lura da wannan tsangya akwai tsohon Alkali Mamman Nasir, Alhaji Bashir Tofa, Farfesa Mustapha Isa Ahmad, Farfesa Shehu Musa Alhaji Farfesa Sule Bello da kuma Farfesa Darfesa Dahiru Yahaya.

Sauran ‘Yan kwamitin sun hada da wani a Fadar Sarkin Kano Mai girma Sanusi II da kuma Mansur Ahmed, Tajuddeen Dantata, Ibrahim Haruna, Alhaji Muhtari Hassan da Alhaji Muhtari Maitama.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel