Aikata baɗala a gidajen kallon kwallo: Sarkin Kano ya baiwa Daurawa muhimmin aiki
Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya umarci shugaban hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa da ya binciko hakikanin gaskiyar zarge zargen da ake yadawa a gari na cewar matasa na tafka ta’asa iri iri a gidajen kallon kwallo a jihar Kano.
Jaridar Puncj ta ruwaito Sarkin Kano ya samu rahotannin dake bayyana cewa matasan unguwannin Badawa, Kawo, Sauna da Haye, suna tafka ayyukan masha’a daban daban da sunan zuwa kallon kwallo.
KU KARANTA: Wani jami’in Dansanda ya rasa ransa a yayin wani hari da yan bindiga suka kai Ofishin Yansanda
Mazauna unguwannin ne suka kai korafi ga Sarkin, inda suka ce wani gidan kallon kwallo da wani attajiri, Auwalu Sankara ya bude ya zama tashar yan iska, inda matasa bata gari ke sheke ayarsu son rai ba tare da kwaba ba.
Shugaban mazauna unguwannin, Mohammed Al-Hassan ya bayyana cewa gurbatattun matasa sun mayar da gidan kallon kwallon wata mafaka da duke siya da siyar da kwayoyi da sauran kayan shaye shaye.
Da yake tattaunawa da tawagar mazauna unguwannin, Sarki Muhammadu Sunusi II yay aba da kokarin da suke yi na sanya idanu tare da kuma tabbatar da zaman lafiya a unguwanninsu, sa’annan ya basu tabbacin hukumar Hisbah zata kamo duk masu hannu cikin lamarin.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng