Za a gurfanar da tsohon gwamna Shema a kotu bisa badakalar kudin SURE-P naira 5.7bn

Za a gurfanar da tsohon gwamna Shema a kotu bisa badakalar kudin SURE-P naira 5.7bn

- Za'a gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema a kotu bisa badakallar kudin SURE-P

- Hukumae EFCC tace Shema ya cire kudin ne daga asusun SURE-P lokacin daya matsayin gwamnan jihar Katsina

- Sauran wanda suka taimaka masa cire kudin sun hada da Alhaji Sani Hamisu Magana, Alhaji Lawan Rufa'i da Alhaji Lawan Dankaba

Ana zargin tsohon gwamnan Katsina, Ibrahim Shehu Shema dayin kaka gida akan kudin SURE-P sama da 7.5bn. EFCC tana zargin tsohon Gwamnan jihar Katsina Alhaji Ibrahim Shehu Shema dayin kaka gida akan kudin SURE-P wanda yawan su yakai N5,776,552,396.

Za a gurfanar da tsohon gwamna Shema a kotu bisa badakalar kudin SURE-P biliyan 5.7bn

Za a gurfanar da tsohon gwamna Shema a kotu bisa badakalar kudin SURE-P biliyan 5.7bn

Tsohon gwamnan ya bayyana a gaban Justice Babagana Ashgar na babbar kotun Katsina a ranar 23 ga Afrilun 2018. EFCC ta bayyana cewa Shema ya cire kudin ne daga asusun SURE -P a lokacin da yake kan kujerar mulki.

DUBA WANNAN: Atiku ya bayyana rashin amincewa da kalaman Buhari a kan matasan Najeriya

Takardar da aka tura masa tana dauke da jawabi kamar haka, "Alhaji Ibrahim Shehu Shema a yayin da kake kan kujerar mulki a 17 February 2014 a karkashin iko na wannan kotu cewar ka ciri kudi N502,216,400 daga asusun SURE-P wanda diban wannan kudi ba da niyyar aikata abinda aka tanade su domin shi ba ya sabawa doka sashi na 15(2) (d) na haramta diban kudi 2011. Sannan za ai maka hukunci da sashi na 15(3) kamar yanda doka ta tanada."

Tsohon gwamnan ya fara fuskantar hukunci a babbar kotun ta Katsina dangane da diban sama da 11bn daga asusun jahar Katsina.

Wadanda suka taimaka masa sun hada da kwamishina Alhaji Sani Hamisu Magana da kuma tsohon sakatare na dindindin na hukumar Alhaji Lawai Rufa'i da tsohon chairman na (ALGON) Katsina Alhaji Ibrahim Lawan Dankaba.

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel