Yadda jirgin sama dauke da gawar tsohon gwamna ya yi hatsari tare da hallaka mutum 13 a Legas

Yadda jirgin sama dauke da gawar tsohon gwamna ya yi hatsari tare da hallaka mutum 13 a Legas

Sashen binciken hadurra (AIB) ya saki rahoton binciken kwakwaf da ya gudanar a kan hatsarin jirgin sama da ya ritsa da jirgin dake dauke da gawar tsohon gwamnan jihar Ondo, Mista Olusegun Agagu.

Jirgin, kirar Embraer 120 ER dake da lambar rijista 5N-BJY, ya yi hatsari ne a filin tashi da saukar jirage na Murtala Muhammed dake Legas, a ranar 3 ga watan Oktoba na shekarar 2013 tare da hallaka wasu mutane 13 da jikkata mutum bakwai.

Yadda jirgin sama dauke da gawar tsohon gwamna ya yi hatsari tare da hallaka mutum 13 a Legas

Yadda jirgin sama dauke da gawar tsohon gwamna ya yi hatsari tare da hallaka mutum 13 a Legas

Kwamishinan a AIB, Injiniya Akin Olateru, ya dora alhakin abkuwar hatsarin jirgin a kan sakacin matukan jirgin.

DUBA WANNAN: An gano gawarwakin 'yan sanda 6 da aka kashe jiya a Benuwe

Kwamishinan ya ce bai kamata matukan jirgin su tashi jirgin sama ba bayan ya nuna alamar akwai matsala injinsa ba.

Wani rahoton hatsarin jirgin sama da AIB ta fitar, shine na kamfanin Westlink da ya faru a kauyen Matseri dake karamar hukumar Bunza a jihar Kebbi ranar 11 ga watan Agusta, 2014.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel